Masana da dama a kwallon kafa na ci gaba da sharhi kan fitar da kasar Faransa daga gasar kasashen Nahiyar Turai ta 2020.
KARANTA: Kasuwar 'yan kwallo, makomar Sergio Ramos da Gareth Bale
Sun bayyana wasu dalilai guda biyar da suke ganin sune suka janyo aka cire Fraansa daga gasar.
Abubuwan da suka faru a wasannin da suka gabata tsakanin Netherland da Greece da kuma tsakanin Belgium da Portugal mai rike da kwofin ya bai wa Switzerland kwarin gwiwar cewa za su iya cinye tawagar Faransa.
Duk da cewa ita ce ke rike da kofin duniya kuma take a matsayi na biyu na jerin kasashen da suka fi ko wadanne kyau a duniya, amma hakan bai hana a cire su daga gasar ba.
Wata dabara da suka kara amfani da ita kuma shi ne hana Faransa taka ledar da suka saba yi a lokutan da suke buga wasansu, salon da Faransa ke yi shi ne na kai kora ta gefunanta da kuma taba kwallo da take yi a cikin hanzari.
Switzerland tayi wata dabar Inda ta rika take manyan ‘yan wasan Faransa a matsayin wata dabarar wasa da za ta fusata ‘yan wasan Faransa da ita, ta rika take ‘yan wasa irinsu Pogba da Rabiot da sauransu.
Farke kwallayen da Switzerland ta rika yi akai-akai ta kara kashewa Faransa jiki, hakan ya sanya su kokarin gwada kwallon da ba ita suka saba yi ba ta, wanda kuma itama ta ki yiwuwa.
Kwarin gwiwar da Switzerland ta samu bayan ta fara farke kwallonta ya sanya ta jin cewa za ta iya cire Faransa daga gasar Euro kamar yadda ya faru.
Wasa daya Faransa ta yi rashin nasara a cikin wasanni 17 da ta buga a gasar kasashen Turai da ta cin kofin duniya, wasan da Portugal ta cinye su a 2016.
Wannan dalili ya sanya mafi yawan masu sharhi da sashen hausa na BBC ta yi magana da su, suka bai wa Faransa nasara a wasan.