Muhimman shan ruwan rake ga jikin mata masu juna biyu.
KARANTA: Abincin Da Mata Masu Ciki Zasu Ringa Ci
KARANTA:Shawarwari Da Likitoci Suka Baiwa Mata Masu Ciki Da Wanda Suke Goyo
KARANTA: Hadin Matse Gaba Da Karin Dandanon Jima'i
Duk inda ka hadu da gungun mutane suna zaune ana ta yada zantuka ba tsayawa, sannan baki kuma na ta motsawa, to ina tabbatar maka cewa ana shan rake a wannan wuri.
Ko da yake sau da yawa, akan dan daga wa mai shan rake kafa a bashi uzuri saboda ganin yakan shiga wani hali na zautuwa idan ba a taro shi ba musamman idan anyi dace da raken mai zakin gaske.
Sai dai kuma wani hanzarin ba gudu ba, rake na da matukar amfani a jikin mutum wanda da yawa ba su sani ba.
Ga amfanin da rake take yi a jikin mutum.
1. Rake na kara karfin kashi domin tana dauke da sinadarin ‘Carbohydrates’.
2. Rake na dauke da sinadarin ‘Vitamin A’ wanda ke kara karfin ido.
3. Shan rake na kare mutum daga kamuwa da zazzabi musamman idan aka matso ruwan aka sha.
4. Rake na hana lalacewan kumba,karyewa ko canza kala.
5. Rake na sa rauni ya warke da wuri.
6. Yana kuma taimakawa wajen samun kaifin kwakwalwa.
7. Shan ruwan rake na taimakawa wajen kawar da warin baki da lalacewar hakora
8. Shan rake na kwara da matsalar rashin haihuwa ga matan da ke fama da wannan matsalar, yana kuma bunkasa girman jinjiri a cikin uwar sa sannan yana hana mata masu ciki yin bari.
9. Rake na taimaka wajen hana jiki ya nuna tsufa da wuri.