Masana sun bawa mata shawara akan irin nau'in abincin da ya kamata su ringa ci domin samun lafiyar su da kuma ta abinda ke cikin su.
KARANTA: Shawarwari Da Likitoci Suka Baiwa Mata Masu Ciki Da Wanda Suke Goyo
KARANTA: Hadin Matse Gaba Da Karin Dandanon Jima'i
KARANTA: Amfanin Shan Rake Ga Mata Masu Juna Biyu
Ita dai mai ciki abinda gangar jikinta yake bukata sune kamar haka :
(1) Hutu tare da kwancyar hankali.
(2) Ta yawaita cin ganye (Kayan lambu) da kuma 'Ya'yan itace.
(3) Ta rika motsa jiki lokaci lokaci domin jinin jikinta ya rika zagawa sosai.
(4) Ta rika shan shayin ganyen Na'a-Na'a domin samar da Qarfin jiki da kuma Kaifin basira ga jaririnta.
(5) Ta rika amfani da Zuma domin samar da kuzari da kuma riga-kafi gareta da kuma jaririnta daga chututtuka.
(6) Idan lokacin haihuwarta ya kusanto ta nemi dabino danye nunanne (irin wanda ake kira Siki) ta rika yawan cinsa. Idan bata sameshi ba, koda busashen ne ta rika amfani dashi.
(7) Shan dafaffiyar garin hulba shima yakan yi amfani ga masu tsohon ciki. Yakan bama mahaifar Mace karfin turowa jaririn idan lokacin fitarsa yayi.
Ki rika shafa Man Tafarnuwa ko man Jirjir ko man Habbatus sauda domin magance ciwon Qafa.
Wadannan duk ba zasu chutar da mai ciki ba. Koda shansu akayi.