YANZU-YANZU: Sojoji sun kama wasu yan boko haram a Kano


Rundunar Soji Ta Tabbatar da Kamun Wasu Yan Kungiyar Boko Haram a Kano. 

KARANTA:Ba zai yiwu a ga wata ranar Talata a Najeriya ba, amma dai a duba: Kwamitin duban wata

KARANTA:Ainihin dalilin da ya sa Buhari ya dakatad da Hadiza Bala Usman

KARANTA:Wata mata mai juna biyu tace cikin ta ya zube lokacin da akayi garkuwa da ita


Rundunar sojin Najeriya ce ta tabbatar da kamun wasu mutane da ake zargin yan ta'addan Boko Haram ne a jihar ta Kano, kamar yadda Legit Hausa suka bayyana. 

Mai magana da yawun runduna ta 3 ta sojojin Najeriya da ke Kano, Kyaftin Njoko Irabor ne ya tabbatar da hakan. 

Sun shiga hannu ne lokacin da sojojin suka kai mamaya Filin Lazio da ke Unguwar Hotoro a cikin garin Kano a ranar Asabar da yamma.

A ranar Lahadi, 9 a watan Mayu ne rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da sumamen da ta kai ga kame wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne a jihar Kano. Mai magana da yawun runduna ta 3 ta sojojin Najeriya da ke Kano, Kyaftin Njoko Irabor ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai amma bai bayar da takamaiman adadin wadanda aka kama ba.

Kodayake, majiyoyi a yankin sun sanya adadin wadanda ake zargin zuwa 10, jaridar Legit ta ruwaito.

An tattaro cewa an kama wadanda ake zargin 'yan ta'addan ne lokacin da sojojin suka kai mamaya Filin Lazio da ke Unguwar Hotoro a cikin garin Kano a ranar Asabar da yamma don mamaye masallaci da wasu gidaje da ake zargin na wasu ‘yan jihar Borno ne da suka tsere daga yankin arewa maso gabas da ke fama da rikicin Boko Haram.

Rahotanni sun bayyana cewa sojojin sun kama mutanen lokacin da suka kutsa Filin Lazio dake yankin Hotoro a cikin garin Kano da yammacin ranar Asabar. Waɗanda aka kama ɗin sun yi koƙarin kai hari ne a wani masallaci da kuma wasu gidaje dake yankin, sai dai rahotanni sun nuna cewa farmakin yazo dai-dai lokacin da musulmai ke shan ruwa bayan sun kai azumi. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post