SHUGABAN KASA BUHARI YA NADA SABON SHUGABAN SOJOJI
KARANTA: An Kashe 'Yan Bindiga 10 A Zamfara
KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Kai Hari A Suleja, Sun Kashe Mutane 3 Sun Sace Wasu 12
KARANTA: An Kashe 'Yan Bindiga 10 A Zamfara
Babban kwamandan hafsoshin sojojin tarayyar Najeriya, Shugaba Mohammadu Buhari ya nada Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon shugaban hafsan sojojin kasar (COAS).
Kafin nadin nasa, Manjo Janar Yahaya ya kasance Babban Kwamandan Runduna ta 1 na Sojojin Nijeriya kuma shi ne Kwamandan mai kula da ayyukan ta'addanci na tayar da kayar baya na rundunar soji a yankin Arewa maso Gabas mai suna Operation HADIN KAI. Wannan nadin ya biyo bayan rasuwar tsohon shugaban sojan wato Attahiru wanda ya mutu a makon jiya a sakamakon Hadarin jirgin sama.
Sanarwa:
Daga
ONYEMA NWACHUKWU
Birgediya Janar
Mai rikon mukamin Daraktan Tsaro
27 Mayu 2021