Yan bindiga sun kashe babban dan Sarkin Kontagora, Bashir Namaska, a gonar mahaifinsa.
An kashe basaraken tare da wasu da ke aiki a gonar a ƙauyen Masuga da ke kan hanyar Kontagora-Rijau a jihar Neja.
Basaraken gargajiyar shine Sardaunan Kontagora kuma ya kasance yana tsaye akan jinyar mahaifinsa, Sarkin, wanda aka ruwaito yana jinya na wasu watanni.
'Yan fashin sun harbe shi a ranar Alhamis yayin da aka garzaya da shi asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsa a lokacin da aka kaishi asibitin, gidan talabijin na Channels TV ne ta ruwaito hakan.
An gano cewa 'yan bindigar sun kuma sace wasu mutane a hanyar su ta barin garin.
Gwamna Abubakar Bello na jihar Neja ya bayyana rasuwar basaraken a matsayin mai sanya zuciya da kuma ta'aziya ga mai martaba sarki da jama'ar masarautar Kontagora kan wannan rashin.
Ya ce, “Abin takaici ne kwarai da jin labarin mutuwar Bashir, musamman a daidai lokacin da ake ci gaba da daukar matakan soja a wasu sassan jihar don tsarkake jihar daga masu aikata laifuka.
“Kamar yadda mutuwar ta kasance mai raɗaɗi, halin da ake ciki zai sa gwamnatina ta tabbatar da cewa an yi nasara a yaƙi da fashi da makami a jihar.
"Ina mika ta'aziyata ga mai martaba sarki da kuma mutanen masarautar Kontagora domin hakika wannan babban rashi ne.
Marigayin ya kasance Darakta-Janar na Hukumar Sayen Kayan Gwamnati ta Jihar Neja tsakanin shekarar 2013 zuwa 2015.
An haifi basaraken ne a shekarar 1979 kuma shi ne Hakimin Kontagora I da Sardaunan Kontagora har zuwa lokacin rasuwarsa.
Tags:
Labaran Duniya