Yan bindiga sun bayyana masu basu makamai kuma suke raba kudin fansa.
KARANTA: An ceto mata 48 da aka yi safararsu a Jihar Kano.
KARANTA: Gwamna Ganduje ya 'yantar da fursunoni guda 123 a Kano
KARANTA: Yadda ake amfani da Zuma wajen gyaran fata
Miyagun 'yan bindiga sun bayyana cewa jami'an DSS da na 'yan sanda ne ke basu makamai suna mugun aiki
Kamar yadda aka zanta dasu, sun ce suna raba kudin fansa ne da jami'an tsaron da ke basu makamai.
Tun dai a 2018, TY Danjuma ya sanar da cewa akwai jami'an tsaron da ke taimakawa ta'addanci a kasar nan. 'Yan bindigan da suka dade suna addabar yankuna daban-daban na kasar nan sun ce suna samun makamai ne daga jami'an hukumar tsaro ta farin kaya kuma su kan raba kudin fansa tare ne idan sun karba.
'Yan ta'addan sun sanar da sashin Hausa na Deutsche Welle a wani rahoto da suka fitar na cewa suna aron makamai ne daga jami'an tsaro farin kaya kuma suna raba kudin da suka samu, Vanguard ta wallafa.