Yadda Zaki Kula Da Lafiyar Nonon ki Da Kanki Batare DA Kinje Asibiti Ba



YADDA ZAKI DUBA LAFIYAR NONONKI DA KANKI CIKIN SAUKI A GIDA BA TARE DA KINJE ASIBITI BA


KARANTA: Mata shin sau nawa kuke duba lafiyar farjinku a rana, ga wasu hanyoyi da zasu taimaka muku


KARANTA: Yadda Zaki Sa Gabanki Yayi Damshi, Koda Kin Haifi Yara Goma, Mijinki Zaiji ki Kamar Amarya


KARANTA: Rashin Sha'awar Namiji a wajen mace da yadda zaki magance Matsalar


Yanada kyau kowanne wata kina duba nononki domin cigaban lafiyar ki. Zaki iya zabar lokaci duk wata ko kinayi kwana biyar kafin al'ada ko bayan kwana uku zuwa biyar bayan period.

A turance ana kiran wannan hanya (breast self examination) ma'ana  yadda zaki duba lafiyar nononki da kanki. Wannan hanya tanada matukar muhimmanci domin ta haka ne kawai zaki iya saurin gano wani 'kari a nonon ki ko ciwon daji mai kama nono wato 'breast cancer' a turance. Wannan hanya zata taimaka wajen gane canji ko matsala jikin nonon ta yadda za'a dauki mataki da wuri, saboda ba wani gwaji wanda zai iya gano cancer a nono cikin sauri fiye da wannan hanyar.

Masana kiwon lafiya na Nono sun yarda cewa duba nononki duk wata tare da bin wasu hanyoyin zai taimaka wajen gano matsala da wuri.

Shekaru da yawa ana ta muhawara akan amfanin breast da yadda mace zata kula dashi wajen saurin gano cancer da taimakawa wajen rage yawan mutuwa da ake samu sakamakon dajin nono.

Masana kiwon lafiyar nono sunyi amanna cewa duba lafiyar nono duk wata ya nada matukar mahimmanci wajen gano cancer nono musamman idan aka hada da zuwa wajen likita domin dubawa akai-akai sannan da yin wasu gwaje-gwajen irinsu MRI, Mammography da Ultrasound. Duka wadannan hanyoyi akwai yadda akeyin su tare da alfanunsu.


Yadda ake duba lafiyar nono a gida

Akwai matakai biyar (5) na yadda akeyi gasu Kamar haka:

(1) Mataki na farko, Zaki cire rigarki sannan ki tsaya kina kallon kanki babban madubi na tsaye. 

Zaki tsaya a tsaye sannan ki kama kugunki, Abubuwan da zaki kula sune: Yanayin girmansu ya canza?, shape dinsu da kalar su, akwai kumburi ko babu.

Idan kikaga daya daga cikin abubuwan da zan lissafa kiyi saurin tuntubar likitan ki:

-Lotsawar nono, burtsowa, motsewa ko yaushi.

-Kan nono idan ya canza waje da aka saba ganinsa, ko ya fada ciki a maimakon waje.

-Ciwo, kuraje, dadewa ko gyambo ko kumburi.

(2) Mataki na biyu, Sai ki daga hannayen ki sama ki rike 'yan yatsunki sannan ki kara duba abubuwan dana lissafa a mataki na daya.

(3) Mataki na uku, Kina dai tsayen kina kallon madubi, ki duba kiga ruwa yana futowa daga jikin nono idan yana futowa ki kula wace colour ne, fari kamar madara ko yellow ne ko kamar jini yake.

(4) Mataki na hudu, Sai ki kwanta a kasa ko gado sannan ki saka pillow a kafadar ki.

-Kiyi amfani da hannunki na dama kina taba nonon hagu kina latsawa kina zagayawa kina tabawa ki tabbata kin zagaya kin latsa ko ina da 'yan yatsunki.

-Sai ki kara maimaita haka da hannunki na hagu ki duba nonon dama ki tabbata kin taba ko ina.

(5) Mataki na biyar, Zaki maimaita mataki na hudu ne amma a tsaye ko zaune sannan zaki iya shafa man zaitun ko wani mai domin kiji santsi don saurin tantancewa.

Karki tada hankalinki dan kinji wani kululu, mata da yawa yana futo musu wanda ba cancer bane irin wannan za'a iya cire shi ko a zukeshi.

-Sannan wasu lokutan ana samun hormonal changes wanda zai saka hakan.

-Zaki tuntubi likitan ki domin karasa sauran gwaje-gwaje dan tabbatarwa da sannin hanyar magancewa.

Ku tura zuwa ga yan uwa domin wayar da kansu


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post