Yadda ake amfani da Zuma wajen gyaran fata



Hanyoyin da ake bi ayi amfani da Zuma domin gyaran fata tayi kyau. 


KARANTA: Wannan hadin shine ake kira da hadin 'yar gata, matan aure zalla

KARANTA: Idan kina shan ruwan kubewa mijinki bazai taba kaurace Miki ba

KARANTA: Yadda ake amfani da citta da albasa wajen gyaran gashi


Assalam Alaikum warahmatullah wabarakatuh! 

Barkanmu da sake saduwa daku a wannan lokacin a cikin cigaba da shirye_shiryen mu na duniyar ilimi da labarai. Yau ma nazo muku da wani sirri wanda ya kamata ku sani musamman mata domin zai muku amfani sosai. 

A cikin wannan rubutun namu na yau zakuji sirrin amfani da Zuma wajen gyaran fata. 

zuma tana da matukar mahimmanci ga mace mai san gyara fatarta. Zuma tana karawa fata damshi da sheki, sannan tana taimakawa gun kashe kurajen fuska.

Ga hanyoyin da ake bi domin amfanin da zuma a gyara fata. 

(1) ki samu zuma da kirfa (cinnamon) sai ki Hadesu ki shafa a fuskarki na tsawon minti 10 zuwa 15 sai ki wanke da ruwan dumi, wannan hadin yana maganin duk wata cuta na fata har irinsu kyasbi da maker kuma yana sa fata tayi sheki da kuma taushi. 

(2) ki samu zuma da lemon tsami ki hada su waje daya ki shafa a fuskarki. Kibar shi na tsawon minti 40 zuwa 1hr sai ki wanke. Yana cire kuraje da tabo sannan yasa fuskarki tayi sumul (smooth) da sheki.

(3) ki hada zuma da nono (yoghurt)mara flavor, sai ki shafa a fuskarki na tsawon 20mins. Yana saka fata tayi kyau, kuma yana cire kuraje da tabo a jiki.



Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post