Matar ta haifi ‘yan mata biyar da maza hudu, in ji ma’aikatar.
KARANTA: An gargadi mata da su daina aske gashin gaban su, domin hakan yana jawo matsala ta kiwon lafiya
KARANTA: Maza masu dogon hanci sunfi girman azzakari, masana kimmiya
Wata mata daga kasar Mali wacce ta haifi jarirai tara - wadanda aka fi sani da nonuplets - na cikin koshin lafiya duk da matsalolin da aka fuskanta a yayin haihuwar.
Yaran za su bukaci kulawar likita har na tsawon watanni uku, in ji mai magana da yawun asibitin Casablanca inda matar ta haihu ya fada wa dpa da yammacin ranar Laraba.
An tura ta zuwa asibitin da ke Morocco a Karshen watan Maris.
Yaran suna cikin koshin lafiya amma har yanzu akwai hadari a kansu, in ji kakakin Abdul Kuddus Hafsi.
Matar ta haifi ‘yan mata biyar da maza hudu, in ji ma’aikatar.
Jarirai daga masu juna biyu da yawa galibi ba duka suke rayuwa ba saboda ana haihuwarsu da wuri.
Hafsi ta ce matar daga kasar Mali tana cikin mako na talatin da haihuwa lokacin da ta haihu.
Wata mata Ba'amurkiya ta mallaki tarihin Guinness World domin mafi yawan yaran da ta haifa a lokacin haihuwa daya domin sun rayu.
Nadya Suleman ta haifi jarirai takwas - octuple - a shekarar 2009. (dpa / NAN)
Akwai ma'aikatan kiwon lafiya 35 da suka halarci haihuwar ta bangaren tiyata, in ji shi.
Likitocin sun sami damar dakatar da zubda jini tare da tseratar da rayuwar uwar da dukkan yaranta Tara.
Source: premium time Nigeria