Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ta bukaci tsige Buhari daga mulkin.
KARANTA: Idan kasan bakada aure kar kayi wannan hadin
KARANTA: Matasa Sun Fara Shirin Karbar Mulkin Najeriya a shekarar 2023
Baba-Ahmed ya ce Najeriya na matukar neman shugabanci a wannan lokaci saboda haka ana bukatar aiki a zahiri maimakon magana ko kuma yiwa jama’a alkawuran da ba’a cikawa.
Jaridar Muryar 'Yanci ta rawaito cewa Mai magana da yawun kungiyar Dattawan ya ce 'yan Majalisu na da hurumin nazarin halin da kasa ke ciki da kuma dubi akan abinda gwamnati tace tana yi da kuma tanade-tanaden da kundin tsarin mulki yayi domin daukar mataki akai.
Baba-Ahmed ya ce muddin Buhari ya gaza sauke nauyin da ke kan sa, shi bai ga dalilin da zai sa Majalisa ba za ta dauki mataki akan shi ba.
Tsohon babban Sakataren gwamnatin Najeriyar yayi tambaya inda ya ke cewa a shekaru biyu da suka gabata babu wani abinda shugaban kasar ya yi da zai karfafa gwiwar jama’a wajen kare rayukan su, saboda haka babu dalilin da zai sa ba za a tsige shugaban ba idan ya gaza.
Baba-Ahmed ya ce abin takaici Najeriya ba ta da Majalisar da ke da kishin kasa da kuma halin da ake ciki ba. (RFI)