Matasa Sun Fara Shirin Karbar Mulkin Najeriya a 2023.
KARANTA: Abubuwa Goma 10 da bai kamata miji ya fada wa matarsa ba
KARANTA: Har da tsohon Shugaban kasa Abdulsalam Abubakar kan zargin daukar nauyin ta'addanci
Matasa daga sassa daban daban na Najeriya sun gudanar da gangamin karbar mulki daga hannun dattawa.
Yayin da shekara ta 2023 ke kara kusantowa, matasa sun dage, inda suka ce suna da lakanin magance matsalolin da kasar ke fuskanta har in sun sami madafun mulki daga hannun wadanda suka ci zamaninsu dana ‘ya’yansu suke kuma cin na jikokinsu.
A hirar su da Muryar Amurka matasan sun bayyana cewa, a shirye suke su kwace mulki a hannun wadannan tsofafin. Bisa ga cewar su, duk cigaban da aka samu a Najeriya, matasa ne suka cimma. Ko a lokacin Shugaba Muhammadu Buhari, da tsohon shugaba Yakubu Gowon da ya hada kan Najeriya kuma ya ja yakin basasa, duk suna cikin kuriciyarsu ne a lokacin.