Ko Kunsan Ranar da ake neman Lailatul Qadri, karanta karin bayani


DAREN LAILATUL QADRI YAUSHE AKE NEMANTA?


KARANTA:Shin zamu iya yin jima’i da daddare muyi wanka kafin muyi sahur?

KARANTA:Hikimomin da azumi ya kunsa

KARANTA:Lokutan da ake karbar Adduar mai azumi


Daga Sahabi Abdullah bin Umar Allah ya kara masa yarda yace; wasu mutane daga cikin sahabban manzon Allah sunyi mafarkin an nuna musu lailatul qadr acikin bakwai din karshe na watan ramadhan, (sai suka labartawa manzon Allah), sai manzon Allah yace "Naga mafarkin ku gabadaya ya hadu akan bakwai din karshe, to duk wanda zai nemeta (lailatul qadr) to ya nemeta acikin bakwai din karshen".

البخاري ٢٠١٥ مسلم ١١٦٥

 Awata ruwayar kuma ya sake cewa "ku nemi lailatul qadr a goman karshe, duk wanda yayi rauni ko kuma ya gaza to kada yayi sake a bakwai din karshe". Muslim 1165.

 Hakika manzon Allah ya kasance yana kara qaimi wurin ibadah acikin wannan wata mai albarka dan neman lailatul qadr, an ruwaito cewa ya taba yin i'itikafi sau daya a goman farko saboda nemanta, sannan yayi a goman tsakiya fiye da sau daya, sannan ya dawwama yanayi goman karshe kuma yabada umarnin a nemeta acikinsa kamar yadda yazo a hadisin Nana Aisha, yana cewa "Ku nemi lailatul qadr a witirin goman karshe na watan ramadhan".

 Manzon Allah ya kasance yana umarni da Neman lailatul qadr acikin wutiri na cikin goman karshe, kamar yadda yazo a cikin hadisin Ibnu Abbas Allah ya kara masa yarda "Ku nemi lailatul qadr a goman karshe na watan ramadhan acikin kwana taran da suka rage, da bakwai din da suka rage da kuma biyar din da suka rage". Bukhari 2021.



Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post