Abokaina sun yi mini ba'a da dariya a lokacin da na fara zuwa aikin leburancin a wajen masu gini. Wata daliba da ta gama karatu a UNIBEN.
Karanta -Ni mace ce mai matsananciyar sha'awa maziyyi yana yawan fitomin ta gabana
"Ba na son tambayar mutane komai, don haka, duk lokacin da naga banida Ko sisi, sai na tafi zuwa wurin aikin ginin. A nan ne zan yi aiki a biyani N2000 na ladan aikin da nayi ," in ji kyakkyawar Jennifer Efemonghe a yayin wata tattaunawa da ta yi da Jaridar Legit.
Karanta -Zamuyi ramuwa akan dukkan wani makiyayi da aka kashe a Kudu maso Gabas, Miyetti Allah
Ta ci gaba da bayanin cewa tun lokacin da take zaune a Legas, inda take zaune tare da iyalinta, ta kan yi fafutukar neman halak a kasuwar Gatankowa - kasuwar da ake sayar da kayayyakin da ake amfani da su na yau da kullum. Yarinyar mai shekaru 20 ta bayyana cewa kawayenta sun yi mata ba'a da dariya a lokacin da ta fara fafutukar neman na kanta amma hakan bai tashi hankalin ta ba, kuma bataji rashin kwarin gwiwa ba.