Illolin Tashar Arewa 24 Da Ire-Iren Ta


 Illar Tashar Arewa Da Ire-Iren Ta


KARANTA: Yadda Zaku Magance Matsalar Kansar Nono Da Ganyen Gwaiba

KARANTA: Wannan magani ne na Basur sosai Indai an hada shi za'a warke

KARANTA: Matashi zai Fara tattaki da kafar sa daga katsina Zuwa kaduna domin bayyana soyayyarsa ga Rahma Sadau


Gabatarwa: 

Muhammad Umar Baballe. 

   <Mu Kori Yaɗa Ɓarna>

Assalam Alaikum warahmatullah wabarakatuh! A wannan rubutun namu na yau zamu kawo muku illolin kallon tashar Arewa 24. 


"Haƙiƙa wannan tasha aba ce wacce take da matuƙar illa da kuma tasiri wajen ruguje tarbiyyar yara a cikin gidajen su a sauƙaƙe"


"Eh tabbas bawai arewa ita kaɗai ce tasha ba wacce take yaɗa irin waɗannan shirmen, amma muma abinda yasa za muyi magana akan ta shine, an jingina ta da sunan arewa, sannan kuma itace tashar da Hausawan mu suka fi ta'ammuli da ita"


"Nasan waɗanda suke goyon bayan wannan hatsabibiyar tashar bazasu taɓa riskar illar da take cikinta ba, sabida idanunsu ya rufe a cikinta su kansu sunyi fana'iy acikinta, amma mu da muke a waje-waje gareta, tabbas mun tsinkayo illar da take ɗauke da ita kuma muke kira ga jama'a da su nisanceta"


"Yanzu azumi yazo, su kuma sun sake zowa da sababbin shirye-shirye domin su shagaltar da jama'a daga ambatõn Allah ta'ala" 


"Acikin sati, kowace rana akwai irin shirin da suke haskawa domin su shagaltar da yara wani lokacin ma har manyan, babu ranar da zata zo ta koma basu saka shirin da zasu ɓatawa yaran mu tarbiyya ba, kai wallahi takai-ta-kawo ma, yanzu wasu yaran har sun haddace ranekun da ake haska fim kaza da fim kaza, irin haddar da basu yiwa alƙur'ani irin ta ba" 


"Ada can baya, idan aka taso yara daga makaranta, bayan sun zo gida, sukan yi bitar karatun su da aka koya musu a makarantar, wani lokacin ma iyayen nasu sune suke ɗora su akan hakan"


"To amma yanzu, zuwan wannan mashiririciyar tashar, tasa yara daga sun dawo gida bayan magriba sai kaji suna a kunna musu kallo domin su kalli raye-raye da Na-naye, wanda ake gudanarwa a cikin wannan tashar"


"A maimakon su dinga yaɗa abinda yake faruwa a Arewacin Nigeria, ko su dinga sanya shirye-shirye masu amfani ga rayuwar jama'a, saidai su dinga sanya abinda zai lalata tarbiyyar ƴa'ƴan mu, ta yaya bazamu kira wannan tashar da suna hatsabibiyar tasha ba?"


"Wallahi wannan abinda kuke sanya wa, ba gyaran al'umma kuke ba, to ai Naji wasu daga cikinku suna cewa ai wa'azantarwa suke yi a hakan, SubhanAllah! To daman ana wa'azantarwa da yin rawa ne, ko kuma ana nishaɗantar da mutane ta hanyar lalata wa jama'a tarbiyya ne?"


"Wallahi Allah wadaran nishaɗin da aka same shi ta hanyar saɓawa Allah maɗaukakin sarki, domin tabbas babu alkhairi acikin duk abinda zai iya janyo mana fushin ubangijin mu Allah komai daɗinsa"


"Muna daɗa tunatar daku cewa, bafa wai tashar ku ce kaɗai muke Allah wadai da ita ba, wallahi muna yin tir da ire-iren wannan tashar taku wacce zata ke ruguza mana tarbiyyar ƴa'ƴan mu"


Bari ma dai na sake tunatar da ku wani abu:


"Shin ko kusan cewa Manzon Allah sallallahu alaihi wasallama yace: mutum ɗaya ya shiryu a dalilin ka, yafi maka alkhairi fiyeda a baka kyautar jajayen raƙuma?, idan kun san da hakan, to ina ƙara yi muku wasici akan hakan, idan kuma baku sani ba, to yau na tunatar daku shi"


"To idan kuwa akace za'a bawa duk wanda ya shiryar da mutum ɗaya gwaggwaɓan lada haka, to shi kuma wanda ya ɓatar da mutane fa, wanda ya rugejewa mutane tarbiyyar su fa?, shi wane irin sakamako za ayi masa?"


Ya Allah ka ganar damu hanya madaidaiciya, Ameen.


Muhammad Umar Baballe

   <Mu Kori Yaɗa Ɓarna>

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post