Gwamna Ganduje ya 'yantar da fursunoni guda 123 a Kano


Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Kano ya 'yantar da wasu fursunoni su 123 a fadin jihar Kano.


KARANTA: Sakon shugaba Muhammad Buhari ga Musulman Najeriya

KARANTA: An Kashe Mayakan Boko Haram A Harin Maiduguri


Ganduje, wanda ya shaida sakin fursunonin daga gidan yarin Goron Dutse a ranar Alhamis, ya ce wannan karramawar ta kasance ne a cikin bikin Sallah karama.

Ya ce an zabi wadanda suka ci gajiyar ne bisa la’akari da irin laifukan da sukai a yayin shigar su kurkukun.

Gwamnan ya bayyana cewa sun yanke shawarar ziyartar gidan yarin ne domin nunawa fursunonin cewa gwamnatin jihar Kano tana sane da kasancewar su a gidan yarin sannan kuma ana daukar su a matsayin ‘yan jihar.

Ganduje ya ce wannan nuna karamci ne don kara kokarin Gwamnatin Tarayya na kara rage cunkoso a gidajen yarin kasar.

Ya shawarci tsaffin fursunonin da su sauya halayensu zuwa rayuwa mai kyau tare da yin addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.

Gwamnan ya kuma ba kowane daga cikin fursunonin da aka 'yanta N5,000 a matsayin kudin tafiya zuwa wuraren da suke.

Tun da farko, Kwanturolan gidan yari na Kano, Suleiman Suleiman, ya gode wa gwamnan kan sakin dubunnan fursunoni da yai tun lokacin da ya hau karagar mulki.

Suleiman ya shawarci fursunonin da aka ‘yanta su guji aikata laifuka don gujewa komawa gidan yarin.

Haka kuma Gwamna  Ganduje ya ziyarci gidajen  marayu da ke babban birni a wani bangare na bikin Sallah.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post