DA DUMI-DUMI kungiyar kwallon kafa ta As Roma ta nada Mourinho a matsayin sabon kocin kungiyar.
Kungiyar AS Roma ta nada Jose Mourinho a matsayin sabon mai horar da kungiyar a shirin da take na tunkarar shiga kakar wasa mai zuwa.
Kulob din ya bayyana hakan ne a ranar Talata, makonni kadan bayan da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta kori Mourinho daga aiki.
"Mun yi farin ciki da maraba da José Mourinho a cikin wannan kungiya ta AS Roma," in ji shugaban kungiyar Dan Friedkin da mataimakin shugaban Ryan Friedkin kamar yadda aka gani a shafin yanar gizon kungiyar.
“Babban gwarzo wanda ya lashe kofuna a kowane mataki, José zai samar da babban jagoranci da gogewa ga wannan kungiya.
Nadin José babban ci gaba ne ga gina kyakkyawar al'ada mai dorewa a duk kulob din. "
KUKARANTA: Da dumi-dumi: 'Yan Bindiga sunyi Barazanar Kashe Wasu daga cikin Daliban da suka Sace a Kaduna.
A nasa bangaren, Mourinho ya bayyana cewa shi da Roma sun yi irin wannan buri. Ya nuna farin ciki da nadin, yana mai jaddada cewa ba zai iya jiran farkon kakar wasa mai zuwa ba.
"Na gode wa dangin Friedkin da suka zabe ni don in jagoranci wannan babbar kungiyar kuma in kasance wani bangare na hangen nesansu," in ji Mourinho.