DA DUMI-DUMI: Boko Haram sun mamaye sansanin sojoji a Borno, sun kori sojoji
‘Yan ta’addan sun mamaye kauyen Ajiri a karamar hukumar Mafa da ke jihar, inda suka farma sansanin sojoji tare da fatattakar sojoji.
Wasu da ake zargin mambobin kungiyar ta Boko Haram ne da safiyar Lahadi sun kai hari kan sansanin sojoji a jihar Borno.
Jaridar Sahara Reporters ta rawaito cewa, ‘Yan ta’addan sun mamaye kauyen Ajiri a karamar hukumar Mafa da ke jihar, inda suka farma sansanin sojoji tare da fatattakar sojoji.
Tags:
Labaran Duniya