Da dumi-dumi: 'Yan Bindiga sunyi Barazanar Kashe Wasu daga cikin Daliban da suka Sace a Kaduna.
An sace Daliban ne su 22 da wani ma'aikaci daga harabar makarantar da ke kan hanyar sa ta Kaduna zuwa Abuja a ranar 20 ga Afrilu kuma cikin mako guda, an kashe biyar daga cikin Daliban.
'Yan bindiga sun yi barazanar kashe sauran daliban da aka sace daga Jami'ar Greenfield dake Jihar Kaduna.
A wata hira da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA), wanda Aminiya ta sa ido, wani shugaban kungiyar ’yan fashin wanda ya bayyana kansa a matsayin Sani Idris Jalingo, ya yi barazanar cewa idan Gwamnatin Jihar Kaduna ko iyalansu ta kasa biyan kudin fansa Naira miliyan 100 tare da ba su babura kirar Honda iri 10 a ranar Talata, sauran daliban za a kashe su.
Jalingo ya ce akwai dalibai 17 da ke hannunsu, wadanda suka hada da mata 15 da kuma maza biyu.
An gano cewa daya daga cikinsu jikan marigayi Sarkin Zazzau na 18, Shehu Idris, wanda ya bayyana da suna Hamza.
Dan fashin ya bayyana cewa tuni iyalan daliban suka tara kuma suka biya su N55 miliyan amma ya kara da cewa sun yi amfani da kudin ne wajen ciyar da daliban.
Ya sha alwashin cewa wannan shi ne kashedinsa na karshe kuma yace gwamnati ko dangin Daliban da suka gaza cimma bukatunsa, za a kashe dukkan daliban.
“Kana magana ne da wadanda suka sace daliban Greenfield. Mun ji kalaman Gwamnan Jihar Kaduna cewa ba zai biya fansa ga ’yan fashi don sayen karin makamai ba,” inji shi.
Da aka tambaye shi ko yana ganin kansa a matsayin dan ta'adda, Jalingo ya yi dariya ya ce: "Ni ba dan ta'adda bane kawai mai neman abinci ne."
Da yake karin haske kan barazanar tasa, dan fashin ya ce: "Idan suka kasa kawo Naira miliyan 100 da sabbin babura kirar Honda 10 da aka fi sani da Boko Haram zuwa ranar Talata, ina tabbatar muku za su yi amfani da manyan motoci don kwashe gawarwakin daliban da suka rage."
Ya gargadi hukumomin tsaro da kada su bata lokacinsu wajen dasa fasinjoji a kan babura, yana mai cewa mambobinsa ba sa zuwa birane don haka kame su zai yi wahala.