Cutar Corona Ta Kashe Fiye da Muatne Dubu 4,000 a rana daya a Indiya



KARANTA:Wata mata ta karya tarihin duniya, ta haifi jarirai 9 a Mali


KARANTA:Kada Ka Sake Cin Gyada Idan Ka Lura Da Waɗannan Abubuwan A Jikinka!


A karon farko, fiye da mutum 4,000 cutar korona ta kashe a rana ɗaya a Indiya Kamar yadda gidan rediyon Bbc hausa suka rawaito.


Akwai fargabar cewa ainihin adadin mace-macen ya fi haka yawa da kuma yawan adadin waɗanda suka kamu da cutar inda ake samun sama da mutum dubu ɗari huɗu a kowace rana.


Masu aiko da rahotanni sun nuna cewa mace-mace na iya karuwa kamar yadda kwayar ta bazu a yankunan karkara wadanda ke da karancin kiwon lafiya.


A ranar Asabar, babban ministan jihar Tamil Nadu a kudancin ƙasar ta Indiya ya sanar da dokar kulle ta tsawon mako biyu kamar yadda jihohi makwabta, Karnataka da Kerala suka ɗauki matakin.


A cikin kwanakin nan dai Indiya tana fuskantar barazana game da yaduwar wannan cutar ta corona virus. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post