Ba zai yiwu a ga wata ranar Talata a Najeriya ba, amma dai a duba: Kwamitin duban wata
KARANTA: Ainihin dalilin da ya sa Buhari ya dakatad da Hadiza Bala Usman
KARANTA:Mace mai haila zata iya yin kowace ibadah a watan Ramadan
KARANTA:Buhari, wasu mutanen basa ganin Alherin Gwamnatina, komai mukayi sai su kushe
Da alamun azumin 30 Musulmai zasu yi a bana, yayin da kwamitin duban wata tace ba zai yiwu a ga wata ranar Talata a Najeriya ba.
Ranar Talata aka bada umurnin duba watan, duk da haka Kwamitin duban wata na majalisar koli ta shari'ar Musulunci a Najeriya ta sanar da cewa ganin jinjirin watan Shawwal ranar Talata, 29 ga watan Ramadana da kamar wuya.
A bayanin da kwamitin tayi ranar Asabar a shafinta na Facebook, ta bayyana cewa an yi hasashen ko wata ya bayyana zai fito ne gabanin faduwar rana, saboda haka ba zai yiwu a ga jinjirin wata ranar Talata a Najeriya ba.
Amma duk da haka jama'ar Musulmi a fadin Najeriya su fita neman jinjirin wata saboda yin hakan ibada ne.
Ranar Talata, 11 ga Mayu ya yi daidai da 29 ga watan Ramadana da ake fara neman jinjirin watan Shawwal na shekarar 1442AH.
Daga Jaridar Muryar 'yanci