An tsinci gawar wani dalibi dan shekara 22 a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kano (KUST), Wudil, Ahmad Abubakar Idiris, kwanaki biyar bayan da aka neme shi aka rasa a makarantar.
Dalibin, wanda ke mataki na 300 a sashin ilimin kimiyyar lissafi kuma mazaunin Abuja, ya bata ne a ranar Asabar lokacin da ya je kasuwar waya (GSM) da ke Kano (Farm Center) don siyan wayar hannu.
An gano gawarsa ne a wurin da ake hakar yashi a Mariri a wajen birnin Kano bayan binciken ‘yan sanda da ya alakanta wani abokin aikinsa wanda ke tare da shi kafin ya mutu.
Da yake zantawa da Jaridar Aminiya, mahaifin marigayin, Abubakar Idris, ya ce ana zargin abokan aikin dansa sune suka kashe shi saboda kudin da ke hannunsa.
Idris ya ce ya samu kira a ranar Asabar cewa dan nasa ya bata kuma ya garzaya Kano daga Abuja a ranar Alhamis bayan ya sanar da ‘yan sanda. Inji jaridar Daily Trust
A cewarsa, lamarin ya faru ne a lokacin da aka turo wa Ahmad wasu kudi domin ya sayi wa dan uwansa wayar hannu.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan Kano, Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kara da cewa an kama mutum biyu da ake zargi.
Ya ce kwamishinan ‘yan sanda a jihar, CP Sama’ila Dikko, ya ba da umarnin a mika karar zuwa sashen binciken manyan laifuka, a Bompai don ci gaba da daukar mataki.
Tags:
Labaran Duniya