Hukumar yaƙi da masu safarar mutane a Najeriya NAPTIP ta ce ta ceto mutum 52 a jihohin Kano da Jigawa da Katsina da ke arewacin ƙasar, waɗanda aka yi yunƙurin safararsu.
KARANTA: Gwamna Ganduje ya 'yantar da fursunoni guda 123 a Kano
KARANTA: Yadda ake amfani da Zuma wajen gyaran fata
KARANTA: Yadda ake amfani da Zuma wajen gyaran fata
Kazalika ta kama mutum huɗu da ake zargi da aikata laifin, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Libya sannan su ƙarasa Turai daga jihohin Imo da Delta da Edo da Ondo da Ogun.
Daga cikin 52, 48 mata ne da kuma maza huɗu, dukkansu 'yan shekara 16 zuwa 34.
Shugaban hukumar na Kano, Abdullahi Babale, ya ce za su tabbatar sun tsaurara sa ido domin ci gaba da kama masu safarar mutane a arewacin ƙasar.