An Cafke Wani Mutum A Sakamakon Yiwa 'Ya'yan Cikinsa Fyade, Harda Yarinya' yar shekara daya
Cikin yaran akwai mai shekaru takwas, shekaru uku, da shekara ɗaya da rabi.
KARANTA: Ina maza masu son Karin ruwan maniyyi, ga magani
KARANTA: Yadda Zaku Magance Matsalar Kansar Nono Da Ganyen Gwaiba
KARANTA: Mata shin sau nawa kuke duba lafiyar farjinku a rana, ga wasu hanyoyi da zasu taimaka muku
Hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) a jihar Anambra ta cafke tare da gabatar da wani mutum mai shekaru 48, Thomas Igbo, da ake zargi da yi wa ’ya’yansa mata uku fyade.
Shekarun yaran nasa sune akwai mai shekaru takwas, shekaru uku, da shekara ɗaya da rabi.
Kwamandan kungiyar a jihar, David Bille, ya fadawa manema labarai a ranar Alhamis a Awka cewa wasu jami'an farar hula a ranar 25 ga Mayu sun ba da rahoton cewa wani Inyamuri yayi wa ’ya’yansa mata uku fyade.
Ya bayyana cewa an gudanar da gwajin lafiya a kan ‘yan matan kuma an gano cewa ana lalata da su, a cewar jaridar Premium Times.
“Lokacin da muka samu rahoton, mun kama wani mai suna Thomas, mai aikin famfo, wanda ke zaune a garin Enugwu-Ukwu a yankin Njikoka na jihar.
“Daga baya ma’aikatanmu na kiwon lafiya sun gudanar da bincike kuma sun gano cewa ana lalata da yaran ta hanyar karfi.
"Wanda ake zargin ya amsa aikata laifin, kuma ba da dadewa ba, za mu kammala bincike sannan mu gurfanar da wanda ake zargin," in ji Billie.
Wanda ake zargin ya yarda cewa ya yi lalata da daya daga cikin ‘ya‘ yan sa mata guda uku, babbar wacce ke da shekaru takwas kuma sau daya ya aikata hakan.
"Na yi lalata da 'yata' yar shekara takwas sau daya, sauran kuma sai kawai na yi amfani da yatsuna don shiga cikin al'aurarsu lokacin da nake musu wanka," in ji shi.
Thomas, wanda ya fito daga yankin Ikoloani Igboetiti na jihar Enugu, ya yi ikirarin cewa ya aikata cikin maye ne a ranar da ya yi lalata da yarinyar.
Mai kula da hukumar kare hakkin dan adam ta kasa, Laura Ugwuanyi, wacce ta je ofishin NSCDC yayin gabatar da wadanda ake zargin, ta nuna damuwar ta kan yadda lamarin fyade ya zama ruwan dare a jihar ta Anambra.
Ta shawarci mazauna garin da su rinka kai rahoton irin wadannan laifukan a duk lokacin da suka san su a matsayin hanyar yaki da barazanar.