Zargin Badakalar N165bn: Ainihin dalilin da ya sa Buhari ya dakatar da Hadiza Bala Usman
KARANTA: Buhari, wasu mutanen basa ganin Alherin Gwamnatina, komai mukayi sai su kushe
An dakatar da shugabar hukumar tashoshin jiragen ruwa a Najeriya NPA, Hadiza Bala Usman, domin bada dama don gudanar da bincike kan wasu kudaden da ake zargin ba'a sanya a asusun bai daya ba.
Wasu takardu da jaridar Legit Hausa ta gani sun nuna yadda Ministan Sufuri yayi zargin badakalar N165bn.
A bisa wasikar da Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya aikewa shugaba Buhari, ya ce adadin kudaden ya kamata ace hukumar NPA ta tura asusun gwamnatin tarayya tsakanin 2016 da 2020 basu kai ba.
A wasikar mai ranar wata, 4ga Maris, 2021, Amaechi ya bayyana cewa a wadannan shekarun, NPA bata shigar da kudi N165 billion ba.
Saboda haka, Amaechi ya bada shawara a gudanar da bincike kan asusun NPA.