Abubuwan da ake so Musulmi ya yi kafin Sallar Idi.
KARANTA: Nayi jima'i a Ramadan, amma bazan iya kaffara ba, Ko zata fadi a kaina?
KARANTA: Mahaifiyata ta Rasu Ana binta Azumi, Shin Zamu iya rama mata?
KARANTA: Ni mace ce mai matsananciyar sha'awa maziyyi yana yawan fitomin ta gabana
Mutumin da ya yi azumin watan Ramadan, an so ya cika azumin da sallar Idi.
Sallar Idi Ibada ce da Allah ya shar'anta a matsayin kammala Ibadah ta Azumin watan Ramadan.
Ba ana yin Sallar Idi ba ne don tunawa da wata ranar haihuwa ko wata nasara da aka samu. Idi Ibadah ce ta yin godiya ga Allah.
Shafin jaridar BBC Hausa ta tattauna da Malam Nura Khalid limamin masallacin Apo a birnin tarayyar Najeriya Abuja, wanda ya bayyana wasu abubuwa da ake son musulmi yayi a ranar Sallar Idi kamar haka:
- Bayar da zakkar fidda-kai ga mabukata.
Zakatur fitr wajiba ce kamar yadda Allah ya farlanta ta. Tafi falala a fitar da ita kafin a tafi masallacin Idi.
Amma an sawwaka a fitar da ita a daren Idi ko kwana biyu ko uku kafin ranar Idi, wato tun a ranar 27 na watan Ramadan musamman ga kungiyoyi ko wakilai da ke tattara zakkar domin raba wa mabukata.
Fitarwa da wuri zai taimaka zakkar ta isa ga mabukata da wuri kafin lokacinta ya wuce.
Allah ya datar damu amen
ReplyDelete