Abubuwan da tsohon shugaban Najeriya Ibrahim Babangida ya ce kan rashin tsaro a gwamnatin Buhari.
KARANTA: Wasu hanyoyi 8 da zaka kiyaye lafiyar maniyyinka
KARANTA: Rashin Sha'awar Namiji a wajen mace da yadda zaki magance Matsalar
KARANTA: An gargadi mata da su daina aske gashin gaban su, domin hakan yana jawo matsala ta kiwon lafiya
Tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya, ya ce samar wa sojoji kayan aiki da horo su ne manyan hanyoyin karya lagon matsalar tsaron da kasar ke fuskanta.
A sakonsa na barka da sallah, ya bukaci 'yan Najeriya da su bai wa gwamnatin kasar haɗin kai domin samar da zaman lafiya da tsaro, yana cewa babbar gudunmawar da jama'a za su bayar kenan daga nasu bangaren don ganin an shawo kan matsalar da ta ki ci ta ki cinyewa.
Tsohon shugaban na mulkin soja ya bayyana matsalar tsaro a matsayin babban kalubalen da Najeriya ke fama da shi a halin da ake ciki, a don haka ne ya bukaci jama'a da su tashi tsaye wajen taimaka wa gwamnati da addu'a, da kuma ba ta hadin kai don kawo karshen matsalar.