Tsohon shugaban fadar gwamnatin Nigeria Malam Abba kyari a yaune yake cika sheakar daya cif da rasuwa.
Shi dai Abba Kyari ya rasu ne a ranar 17 ga watan Afrilu na shekara 2020 sakamakon rashin lafiya wacce ake kyauta zaton cewa cutar corona ce tai sanadin rasuwar sa.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana marigayin a matsayin babban aminin sa na jiki mai kishin kasa.
Shugaba Buhari ya Kara da cewa Abba kyari aminin sa ne tun tsawon shekaru 42 da suka gabata suna tare kafin daga bisani ya zama shugaban ma'aikata a fadar sa.
Shi dai malam Abba kyari ya rasu ne yana da kimanin shekaru 67 a duniya.
Muna Adduar Allah ya jikansa da sauran wanda suka gabata amen.