YAN BOKO HARAM SUN SHIGA KWANA NA 3 SUNA SHEKE AYARSU A GEIDAM



Mayakan Boko Haram Sun Shiga Kwana Na 3 Suna Sheke Ayarsu A Garin Geidam na Jihar Yobe. 


Kwana uku kenan a jere mayakan kungiyar Boko Haram na cin karensu babu babbaka tun bayan kaddamar da hari a garin na Geidam na jihar Yobe ranar Juma’a.


Sai dai zuwa yanzu Gwamnan Jihar, Mai Mala Buni ya yi batan dabo, inda babu tabbacin ko yana jihar ko kuma yana Abuja inda galibi ya fi zama domin jagorancin jam’iyyar APC.


Sai dai bayan ruwan wuta daga sojojin sama wanda ya kori ’yan ta’addan, daga bisani sun sake dawowa garin suka ci gaba da ta’asa.


Akalla Mutum 11 ne ’yan gida daya aka tabbatar da kashe su sakamakon wani abin fashewa da ya tashi a unguwar Saminaka, kusa da sansanin sojoji na Geidam.


Wani mazaunin yankin, Abba Nura ya ce babu wanda zai iya tabbatar da ko sojoji ne ko kuma ’yan ta’addan ne suka tayar da bam din.


"Bayan mun shiga gidansu jim kadan da tsagaita wuta a harbe-harben, sai muka iske gawarwakin mutum 11 da suka mutu"


Sai dai ya ce saboda halin da ake ciki, ba zai yuwu a yi musu jana’iza a garin ba.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post