YADDA ANNABI S.A.W YAKE GUDANAR DA ALWALAR SA

 


SIFFAR ALWALAR ANNABI (SAW)


  •  Farko yana wanke tafukan hannunsa sau uku, tare da yin niyya.

  •  Sannan sai ya kuskure bakin sa ya shaka ruwa sau uku uku (da kanfata uku). 

  •  Sai kuma ya wanke fuskar sa sau uku. 

  • Sannan ya wanke hannayensa zuwa gwiwar hannu sau uku, yana farawa da hannun dama. 

  •  Sai kuma ya shafi kansa da kunnuwansa sau daya. 

  • Sannan sai ya wanke kafafuwan sa sau uku, yana farawa da kafan dama.

  • Yana karanta wannan Addu'ar bayan ya gama alwalla;

 أشهد أن لاإله إلا الله وحده لاشريك له، وأشهد ان محمدا عبده ورسوله، اللهم اجعلني من التوابين واجعلني من المتطهرين"

Ash_hadu an-la'ila ha illallahu wahdahu laa sharika lahu, wa ash_anna Muhammadan 'abduhu warasuluhu, Allahumma j alniy minat_tawwabina waj_alni minal mutatahhirina"

Fassara: 

 Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kad'ai, babu abokin tarayya a gare shi: kuma ina shaidawa cewa Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa ne.Ya Allah ka sanya ni a cikin masu yawan tuba, kuma ka sanya ni a cikin masu tsarkaka.


NB: Ana so duk sanda mutum ya  yi alwallah, ya yi sallah raka'a biyu (Ana kiranta NAFILAR ALWALLA).

Tsokaci:

Ku Sani ya jama'a, ita alwala wata hanya ce ta kankarar zunubai. Amma se ana yinta irin alwallar Annabi (SAW).

Dan Allah idan ka karanta Ko kin karanta ku tura sauran yan uwa domin su amfana


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post