Yadda ake amfani da danyar ciita (ginger) da albasa(onion) wajen Kara tsawo da laushin gashi.
Zan ajiye muku video a Karshen wannan rubutun domin ku kalla ku Kara fahimtar yadda zakuyi.
Idan aka shafa wannan hadin a kan gashi zakuga yadda gashin zai canja cikin Karamin lokaci.
Da farko dai zaku Sami citta danyar ciita wadda muke Kira da ginger, Sannan a Sami albasa mai kyau kwara daya.
Yadda zakuyi shine zaku bare bawon ciitar ku yankata kana-na, sai ku bare albasar itama ku yankata kanana.
Bayan kun yankasu kanana sai ku zuba a cikin blander ku markada, bayan kun markada sai ku dauko abin tacewa ku sami cup Mai kyau ku tace ruwan. Sai ku samin man olive ku zuba Kamar cokali 2 sannan a zuba man lavender (lavender oil) sai a girgiza sosai su hade.
Bayan kun Gama sai a shafa a gashi a barshi na tsawon 1hr sai a wanke, kuyi haka na tsawon kwana 3, kuma duk bayan sati ku ringa yin hakan zakusha mamaki.
Ga video da nace zan ajiye muku.