WASU HALAYE 10 NA MACE YAR LESBIAN



Assalam Alaikum warahmatullah wabarakatuh!

Barkanmu da sake saduwa daku a cikin cigaba da shirye_shirye na wannan shafi mai albarka na duniyar ilimi. A koda yaushe muna yimuku fatan alheri. 

A wannan rubutu na yau zakuji wasu alamomi guda 10 na mata yan madigo, sannan kuma zan ajiye muku video a Karshen wannan rubutun domin karin bayani game da wannan batu. 

Alamomi Da Ake Gane Mace ‘Yar Madigo: 

Akwai alamomi masu matukar yawan gaske wanda ake gani da ma wanda sai su kadai (wato masu yin wannan harkar ta madigo) suke gane kansu. 

Kadan daga cikin wanda muke gani a zahiri sune Kamar haka : 


(1) Masu yin madigo suna da son yin kyauta ta bajinta ga mata musamman wadanda suka gani suna so. 


(2) Abu na biyu shine suna da matukar son yin dinkin riga matsattse me bayyana nononsu.


 (3) Idan sun hadu da mace wacce ta yi musu sun ringa yi ma ta farin ido wurin yi mata magana kenan don son jawo ra’ayinta. 


(4) Suna da son yabawa sura (kyan diri) na mace musamman wacce suke son jan ra’ayinta zuwa harkar.


 (5) kuma suna da son koda kyan  mace fiye da namiji 


(6) Suna da mummunan kishi musamman idan sunga wacce suke so tana mu'amala da wasu mazan. 


(7) mata masu wannan dabi'ar su sam basu damu da yin mu’amala da maza ba, kullum sun fi son su kusanci mace cikin nuna sha’awa. 


(8) Suna da son kwalliya, tsabta da kula da fatar jikin su. 


(9) Suna da son yin mu’amala da kalolin turaruka daban_daban. 


(10) Suna son saka sarka a kafarsu da zobe a yatsar kafar, duk da yanzu kusan an mayar da yin hakan gay amma nasu na musamman ne. 


Wadannan su ne kadan daga cikin alamomin da za a iya gane ‘yan madigo da su, amma ba su kenan ba, Kamar yadda muka fada a farko , akwai wasu alamomin da sai su da ke cikin muguwar dabi’ar ke iya ganewa ko kuma idan an yi la’akari da abubuwan da suke aikatawa da zarar sun hadu a tsakaninsu. Iyaye sai mu kula a duk lokacin da muka ga wata alama makamanciyar wadannan ga yaranmu ko wacce ke mu’amala da yaranmu mata sai mu yi kokari mu yi wa tufkar hanci. 

Ku danna nan ku kalli video domin karin bayani 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post