Rundunar sojin Nigeria ta bayyana cewa dakarunta dake yin aikin samar da tsaro a yankin arewa maso gabashin kasar, sun kashe wasu daga cikin kwamandojin kungiyar ta boko haram da ISWAP su kimanin 18 a Jihar BORNO.
A rahoton da rundunar suka bayyana cewa har da Bukar Gana wanda ake yiwa lakabi da suna Aisha.
Mai magana da yawun rundunar birgediya janar Muhammad Yerima shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai.
Yace yan ta'addan sun fada tarkon dakarun sojin Nigeria ne lokacin da suke kokarin kai wani harin ramuwar gayya a cikin garin Damaskas dake a Jihar BORNO