SOJIN NIGERIA SUN KASHE YAN BINDIGA 5 A JIHAR BENUE


Rundunar sojojin Najeriya sunkashe wasu ‘yan bindigar guda biyar wadanda suka kai hari wani yanki a karamar hukumar Makurdi da ke jihar Benue.

Rahotanni sun ce sojojin sun dirarwa maboyar ‘yan bindiga da ke tsakanin iyakar jihar Benue da ta Nasarawa.

Sun kuma bayyana cewa ‘yan bindigar sun kai hari kan kauyen Anune tun da fari, wani karamin kauye da ke yankin Makurdi tare da kashe mutane a cikinsa.

Wani wanda ya shaida wa manema labarai faruwar lamarin ya ce tun da misalin karfe 9 zuwa 10 na safiyar Asabar suka ga jirgi mai saukar angulu yana shawagi a saman inda aka kai harin, kafin daga bisani motocin ‘yan sanda su isa wurin.

 Yace sojojin sun kutsa kai cikin dajin da ake zargin yan bindigar suke ciki, daga baya kawai sai aka ga sun fito da gawa kimanin guda biyar.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post