HADIN COCUMBER, MADARA DA LEMON TSAMI
Barkanmu da sake saduwa daku a wannan lokacin a cikin wani sabon shirin namu.
A yau insha Allah zakuji wani sirri wanda duk wanda yake yin wannan hadin to zai sha mamaki.
GA YADDA AKE YIN WANNAN HADIN
Idan ka Sami cocumber ka fereye ma'ana a cire bawon sa sai a yanka shi kanana a zuba a mazubi Mai kyau, sai a Sami madarar ruwa Mai kyau Kamar gongoni daya a juyeta a ciki sai a dauko lemon tsami a rabashi gida biyu sai a matse a cikin wannan cocumber, bayan an hade su waje guda sai a juye shi a cikin blander a markada su bayan an markada sai a zuba a cup a sha, awa daya kafin a ci abinci.
Wannan hadin yana inganta lafiyar jiki, karin kuzari, kwanciyar hankali, gyaran fata da sauran su.