SIFFOFIN MATAR AURE TA GARI
Assalamu Alaikum warahmatullah wabarakatuh!
Yau a cikin shirin zakuji wasu alamomi guda 13 na mace tagari, wanda duk wani namiji nagari yadace ace ya samu mace mai irin wannan siffofin. wannan siffofin kuwa sune gasu Kamar haka:
(1) Ita ma'abociyar addini ce da kyawawan ɗabi'a, tana tsayuwa akan abinda ALLAH ya wajabta mata akanta daga bautar sa, tana bin umarnin sa gwargwadon iko kuma tana nesantar hanin sa gwargwadon iko, tana tsayuwa akan dokokin ALLAH cikin yanayi na farin ciki ko bakin ciki, kuma ita ma'abociyar riko da sunnah ce matuƙa.
(2) Tana yiwa mijin ta biyayya matuka da nuna masa kauna, cikin abinda yake ba saɓon ALLAH ba, domin ba'a yin biyayya ga ɗan Adam halittace, cikin saɓawa mahalicci.
(3) Tana nuna soyayya ga mijin ta matuƙa da kulawa, kuma wannan nuna soyayya ga mijin ta yana daga cikin manya manyan dalilan da suke kara karfin soyayya a cikin zuciyoyin su da kuma kara karfin sha'awar juna da dauwamar da kauna da kuma tausayi a tsakanin su akan kaunar da UBANGIJI ya riga ya sanya tsakanin su da tausayi.
Domin ALLAH Yace': Kuma ya sanya kauna a tsakanin ku da jin kai. Sura Arruum 21
(4) Matar aure ta gari ta kasance mai kwaɗayi kara kusantowa ce ga aikata dukkan wani abu da zai kara sadar da ita, ga samun yardar mijin ta, tana kiyaye dukkan wani abu da zai janyo zargi ko rashin yarda tsakanin su kuma tana Addu'a akan haka, idan ta ɓata masa rai sai ta ba shi hakuri har sai ya hakura, in ya dawo ranshi a ɓace sai tayi kokarin kore masa ɓacin rai in, tana gyara kuskuren ta kuma tana karɓar laifin ta.
(5) Ta kasance mai hidima ga Mijin ta, har bakin sa, yan'uwan sa, a lokacin da suka ziyarce ta, tana kiyaye dukiyar mijin ta, ba ta ciyar wa sai da sanin sa, ba ta sadaka da shi sai da izinin sa, sai dai in ya kasance ba ya ba ta abinda zai ishe ta da ya'yan ta to wannan ya zamo lalura sai ta dauki abinci tayi kari ko dukiyar sa yadda zai ishe ta da yaran ta.
(6) Ta kasance mai kiyaye wa mijin ta ya'yan su, da tarbiyyantar da su tarbiyya kyakkyawa na gari.
(7) Tana kiyaye masa mutuncin sa a bayan idon sa baya nan, kuma ba ta raina sa a bayan idon sa ko a tsakanin mata, ba ta magana akan abinda zai janyo zubar masa mutunci ko kima, ba ta yaɗa kuma sirrin sam
(8) Tana masa uzuri da ɗaukar sa mai kuskure da hakurin zama da shi a matsayin sa na ɗan Adam, tana masa yafiya tare da saukin kai a gare shi, ba ta kuma ɗaura masa ciyar da ita ko tufatar da ita ko ba ta abinda bai da ikon sa.
(9) Tana yi wa mijin ta kwalliya, da gyaran jikin ta, da game kanta da gidan ta da kamshi, ta yadda zai samu nutsuwa da ita, yayi farin ciki da kallon ta, ba ta yarda ta zubar da kimar ta ko ta kawar mishi da sha'awar sa ta kasancewar ya dawo gida ya same ta cikin datti ko wari, watakila ma ya dawo ne saboda samun nutsuwa da biyayya ga sunnah Manzo saw, in kuka ga mata sun burge ku ku dawo ga iyalan ku, kasancewar ta cikin datti zai iya jefa shi cikin matsalar aukawa ga wani abu ko neman mata ko rashin runtse idanu.
(10) Tana kokarin tausasa murya wajen magana da shi, tana kokarin kyautata tafiya irin wanda yafi so da burge sa, tana kokarin yin kitso irin wanda yafi burge shi da gyaran gashi, tana kokarin sanya sutura mafi burge shi, tana kokarin amfani da turare iri iri daidai Gwargwadon iko, tana kuma kokarin yi masa abubuwan ba zata na soyayya.
(11) Tana kyautata masa zato tare da taimakon sa cikin ɗa'a ga ALLAH da Manzon sa saw da iyaye da kokarin kara masa nuni akan kyautata musu tare da yan'uwan sa na jini da kuma Musulmai, daidai gwargwado ikon sa, tare da taimako cikin addini ALLAH.
(12) Ako da yaushe tana kokarin nuna mishi soyayya ko da cikin ya'yan su ne tasan salon yadda za ta yi magana da shi yadda zai isar masa da sako har zuciya🙈tasan sunaye da take kiran sa dashi a kowanne irin yanayi anguwa suka fita, ko cikin yara, ko other room🙈😎, ba ta kuma taɓa yarda taji ta yanzu tafi karfin soyayya an bar wa yara kullum kara koyo take da kuma ɗabbakawa.
(13) Ba ta leke, ba ta fita ba tare da izinin mijin ta ba, ba ta barin a shiga gidan sa sai da izinin sa, ba ta CHATTING da maza ko matan banza, ba ta shiga group ɗin banza, ba ta ha'intar mijin ta, ba ta bin bokaye, ba ta azumi na nafila sai da izinin sa, ba ta barin sa ta tashi dare tayi ta sallar nafili, sede a karshen dare su tashi tare, ta yarda shugaban ta ne shi kuma sanadiyyar aljannar ta ne duniya da lahira