NI MACE CE MAI YAWAN SHA'AWA, KUMA KUSAN KODA YAUSHE RUWA YANA KWARANYA DAGA FARJINA
Alaikum warahmatullah! Malam a taimaka a amsamin wannan tambayar
Tambayata ta parko itace:
Macece takasance mai karpin sha'awa kuma koda yaushe takan fidda farin ruwa (mazi) yakan zubo koda tana sallah ne, sannan idan ta kwanta barci takan yawaita mafarki saboda yanayin karfin Sha'awarta. Kuma a duk lokacin da take al'ada Sha'awarta yana kara tsananta sosai.
To tambaya anan shine shin duk lokacin da taga wannan ruwan sai tayi wanka ?
Kuma gameda karpin sha'awarta maimakon taje ta fada sabon Allah zata iya wasa da hannunta don gamsar d kanta, ko kuma nonon ta kodai makamancin hakan?
Saboda tana gujewa sabawa mahallici.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ.
AMSA
Da farko dai Maziyyi baya wajabta wanka.
Maziyyi yana fitowa ne a dalilin motsawar sha'awar Namiji ko Mace.
Maziyyi yana warware alwala amma baya lalata azumi.
A yanayi na yawan fitar maziyyi malamai sunce ya zama dole mutum ya tsarkake al'aurarsa da wajen da maziyyi ya shafa tareda yin sabuwar alwala a duk lokacin da zaiyi sallah.
Idan kuma kika ga maziyi bayan kin gama sallah to zaki wanke muhallin amma bazaki sake sallah ba. Wato idan fitar maziyyin ya yawaita kuma ba kece kike janyo fitarsa ba ta hanyar chating da samari ko kallon hotunan batsa da sauransu, to koda kin fara sallah babu maziyyin saida kika kammala kika ganshi to ba zaki sake sallar ba saboda abin yafi karfinki. Saboda fadar madaukakin sarki
(لا يكلف نفسا إلا وسعها)
Allah baya dorawa rai abun da ba zata iya ba. Amma fa ki sani idan fitar daga gare ki ne to kece ke bata sallarki da kanki. Saboda haka sai kisan mafita, kiji tsoron Allah ki tuba ki daina abubuwan da kike yi masu janyo fitarsa.
Haka kuma idan kikayi sallah da maziyyi ajikinki acikin mantuwa, anan ma zaki wanke ne idan kin tina amma bazaki sake sallah ba.
Idan maziyyi ya fito kuma kikayi sallah batareda kin wanke ba. Malamai suka ce sai kin sake sallah bayan kin wanke.
Saboda shi Maziyyi najasa ne kuma fitarsa yana warware alwala. Amma kuma idan fitar tasa ya kasance koda yaushe hakane ba yanda zaki yi sallah ba tare da kinji ya fito miki ba kuma ya kasance ba kece ke janyowa kanki fitarsa ba to anan kam zaki ci gaba da sallarki kamar yadda muka fada a sama:
(لا يكلف نفسا إلا وسعها)
Allah baya dorawa rai abinda bazata iya ba. Saidai idan kika gama ki wanke gabanki ki wanke wajenda ya taba ko kiyi yayyafi, idan zaki sake wata sallah ki sake alwala saboda alwala kawai yake karyawa baya wajabta wanka.
Akan wanke daukacin muhallin da maziyi ya shafa a jiki da sutura.
Haka kuma za'a iya yayyafi a sutura a bigiren da maziyyi ya shafa kamar yadda yazo a hadisin tirmizi.
(Ibn Qudaamah a littafinsa na Al-Mughni, 1/168).
(Sahihul Tirmizi, 115, Albani ya ingantashi).
(Al-nawawi, sharhin sahihul Muslim, 3/213)
Allah ne mafi sani