NI DA MATA TA MUN YI JIMA'I MUNA DAUKE DA AZUMI MENENE HUKUNCIN ABINDA MUKA AIKATA



Assalamu Alaikum warahmatullah wabarakatuh! 


TAMBAYA 

Ni da matata mun yi jima'i muna dauke da azumi saboda haka menene hukuncin abin da muka aikata?


AMSA

Wa'alakum Salam Warahmatullah Wabarakatuh! 

Azumin ku ya baci idan ba ku san cewa yin jima'i yana bata azumi ba ma'ana kun kasance jahilan da ba su san cewa su jahilai ba ne to zai kasance kadai zaku rama azuminku da kuka bata shi da jima'i bayan watan ramadana, amma idan kun san

[1] cewa yin jima'i na bata azumi sannan kuka aikata jima'in to bayan kun rama azumin sai kun bada kaffara

[2] Wajibi mu tunatar da cewa abubuwan da suke bata azumi sune: 

  •  cin abinci da shan abin sha 
  •  Yin jima'i 
  •  istimna'i (fitar da maniyyi ta hanyar wasa da azzakri ko makamancinsa) 
  •  jin gina karya ga Allah ko ga Annabi (s.a.w) ko ga magajinsa (a.s)  
  • shigar da Kura mai kauri zuwa ga maKogaro 
  •  nitsar da baki dayan kai cikin ruwa 
  •  zama cikin janaba da haila da nifasi har zuwa lokacin kiran sallar asubahi  
  • yin allura da wani abu mai ruwa ruwa  
  • yin amai[3]

 

[1] Idan ya kasance ta hanyar rashin sanin hukuncin mas'ala suka aikata aikin to azumin ya lalace, amma idan ya kasance zasu iya neman sanin hukunci mas'alar to a wannan lokaci za a kidaya su cikin jahilai mukassirai, saboda haka bisa ihtiyadi wujubi kaffara ta wajaba kansu, amma idan ya zamanto basu iya neman sanin hukuncin mas'alar ko kuma tun asali ma basu lura ba ko kuma basu samu yakini ba kan cewa abu kaza na karya azumi, to a wannan lokaci zasu zamanto jahilai kasirai kaffara bata wajaba kansu ba, littafin tauzihul masa'il amai hashiya na na komaini juz 1 sh 927 ms 1659, domin neman Karin bayani ana komawa ga site 3319 mas'ala mai lamba 2668

[2] Tauzihul masa'il mai hashiya na komaini juz 1 sh 935 ms 1678, idan mai azumi cikin watan ramalana ya kusanci matarsa yayi jima'I da ita alhalin yana dauke da azumi to idan ya kasance ya tilasta ta ne kan hakan to wajibi ne kansa ya bada kaffararsa da kaffarar azumin matarsa da ya karya , amma idan ya kasance ckin yardar juna suka kusanci juna to kowanne dayansu zai bada kaffara.

[3] Tauzihul masa'il mai hashiya ta komaini juz 1 sh 891 ms 1572

Allah mafi sani

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post