NA CI ABINCI BAYAN ALFIJIR YA KETO YA MATSAYIN AZUMI NA

 



NA CI ABINCI BAYAN ALFIJIR YA KETO


Tambaya

Assalamu Alaikum Warahmatullah Wabarakatuh! 

Malam jiya bayan na gama cin abinci, sai na samu ashe alfijir ya keto, tun kafin na fara ci, saidai Allah ya sani, na ci ne a rashin sani, ko ya zan yi yanzu ?


Amsa

Wa'alaikum Assalam Warahmatullah Wabarakatuh! 

To malam mutukar ba da saninka ka yi haka ba, to azuminka ya inganta, domin duk lokacin da mai azumi ya yi kokwanton hudowar alfijir, to ya halatta a gare shi ya ci abinci, saboda wanzuwar dare shi ne asali. 

kamar yadda Ibnu-abbas yake cewa : "Allah ya halatta mana cin abinci - a Ramadhana- mutukar mun yi kokwanton hudowar alfijir", sai dai in da zai yi kokwanton faduwar rana to bai halatta a gare shi ya Ci abinci ba, saboda wanzuwar ranar shi ne asali.


Allah ne mafi sani 



Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post