MIJINA YA TAKURA MIN MUN SADU A CIKIN RAMADANA!
Tambaya
Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuh.
Malam yau ina cikin damuwa, saboda na kwanta baccin rana, kawai sai na ji mijina ya danne ni, na yi ta kokarin na kwace amma sai ya ci karfina ya sadu da ni, alhalin muna azumi, don Allah malam a taimaka min da mafita, Allah ya sanyawa zuriyarka albarka
Amsa
Wa'alaikumus salam, warahmatullah wabarakatuh.
To 'yar'uwa mutukar yadda kika siffanta, haka abin ya faru, to babu kaffara akan ki, saboda takura miki aka yi, kuma ba ki da laifi a wajan Allah, amma shi kuwa ya sabawa Allah, kuma ya keta alfarmar Ramadana, kuma dole ya yi kaffara, ta hanyar 'yanta kuyanga, in bai samu ba, sai ya yi azumin sittin a jere, in bai samu dama ba sai ya ciyar da miskinai sittin, kamar yadda ya zo a hadisin Bukari mai lamba ta: 616.
Allah ne mafi sani.