TANADI DAN SHIGA WATAN RAMADHANA
1-Yin murna da farin ciki da shigowar wannan wata mai albarka tare da yin albishir ga sauran musulmai ga shigowarsa kamar yadda Manzon Allah yakeyiwa sahabbansa
2-Tuba ingantacce da nisantar zunubai baki daya,dan kashi watan kana mai tsarkin zuciya da tsarki aiki.
3-Sanin Hukunce hukuncen da suka shafi azumi da aiyukan ibada na watan Ramadhana daga Alqurani da Sunna abisa fahimtar Magabata na kwarai.
4-Nisantar miyagun halaye da aiyuka abin kyama,da mayesu da halaye masu kyau.
5-Yin Himma da Azma da niyyar aiwatar da aiyuka alkhairi masu yawa acikin wannan wata mai albarka.
6-Yiwa kanka tsarin aiyukan alkhairi da kake so ka aikata masu yawa a wannan watan,kamar sauke alqurani da ciyar da masu azumi da kyautatawa mahaifaya fiye da da, da sauran aiyuakan dhaâ
7-Shagaltuwa da Yawaita Ambaton Allah da zikiri da istighfari da Tilawar alqurani da kokarin SANIN ma'anoninsa.
8-Kiyayae sallaah akan lokutanta da kyautata sallah da ikhlasy da cika rukunnan Sallah.
9-Yawaita aiyukan nafila kamar sallolin tarawi da nafilolin dare da na bayan sallah da kafin sallah.
10-Ikhlasy da kyautata niyyar adukkan ibadunka.
Allah ne mafi sani
Ya Allah ka isar da rayuwar mu watan Ramadhana muna imani da kyakkyawar niyya