DA DUMI-DUMINSA IDRIS DEBY YA RASU!
Shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya rasu a wannan Talata 'yan sa'o'i kadan bayan da aka bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a baya-bayan nan.
Rundunar sojin kasar ta Chadi ce ta sanar da mutuwar shugaban, inda ake zullimin ya mutu ne a sanadiyyar raunin da ya samu a "fagen daga" wurin yaki da 'yan tawayen da ke hankoron kwace iko da gwamnatin kasar.
Tags:
Labaran Duniya