James wani bature da ya auri Joy Bishara daya daga cikin yan matan chibok da 'yan boko haram sukayi garkuwa dasu a shekarun baya.
Bayan tsira da wasu daga cikin matan da aka sace sukayi ciki har da Joy Bishara wanda daga bisani ta hadu da masoyin nata James har sukayi aure shekaru 2 da wata shida da suka gabata.
Bishara ta bayyana mijin nata a matsayin jajirtacce, mai kula, mai jin kai da tsoron Allah da kuma yadda yake nuna mata soyayya.
Ta bayyana cewa tana murnar kasancewar su na tsawon wannan lokaci da suka dauka tare a matsayin ma'aurata.