Illolin Yin Wasa Da Azzakari Da Farji




YAYA YAWANCIN KU KUKE JI BAYAN TABA AL'AURAR KU DA NUFIN FITAR DA MANIYYI? SHIN KUN TABA JIN BACIN RAI BAYAN AIKATA HAKAN


Abu ne mai kyau yayin da mutum yaji a ransa cewa yana so ya gamsar da Kansa ta hanyar yin wasa da al'aurar sa domin yajiyar da kansa daɗi ta hanyar fitar da maniyyi. 


ILLAR DA ISTIM'NA'I (MASTURBATION) KE HAIFARWA GA LAFIYAR BIL'ADAMA


Masana a fannin kiwon lafiya sun bayyana cewa, duk sanda bil'adama ya fitar da maniyyi, wahalar da jiki kan yi na dai-dai da gudun kilometer 13 (13km) wasu na iya wannan dabi'ar sau 3 ko fiye da haka a wuni, kunga a nan dole matsaloli su biyo baya kamar ciwon jiki da shanyewar hannaye da kuma rama da rashin kuzari. 


A bisa wannan dai masanan sun tabbatar da wannan dabi'ar na ruguza daukacin tsarin jikin bil'adama.


Masanan har ila yau, sun bayyana cewa wannan dabi'ar kan jawo ciwon zuciya ga mai yin ta. Ya kan jawo rashin karfin gaba. Duk mai wannan dabi'ar yau da gobe zai rasa karfin gabanshi kwata-kwata. 


Har ila yau an tabbatar da cewa duk mai yin wannan dabi'ar lallai ne sai ya kamu da cutar sanyin mara (gonorrhea) wanda kan iya illanta shi.


SHAWAR TA YADDA ZA'A IYA GUJEWA DABI'AR YIN ISTIM'NA'I (MASTURBATION) 

 

(1) Da farko in mutun ya tsinci kanshi cikin wannan dabi'ar kuma yana bukatar dainawa, to, sai ya kudurta a cikinn zuciyarsa cewa zai daina sabili da dabi'ar na da makutar wuyar dainawa muddin ta yi wa mutun katutu.


(2) Mutum yayi kokarin aure idan da hali


(3) Ka daina kadaita a dakinka ko gidanka, ka rika shiga mutane dan mafiyawa kadaita ke sa wasu mutane wannan dabi'ar


(4) A guji shan kwayar da zata tada sha'awar jima'i


(5) A guji yawan kallon ababen da zai tada sha'awa, hoto ko bidiyo, kana a guji yawan zantutukan batsa.


(6) A yawaita jin karatu ko wa'azi a ko da yaushe.


Idan aka kiyaye wadannan abubuwa, in Allah ya yarda mai dabi'ar zai iya dainawa. Allah Ya sa mu dace.



Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post