MEYSA KUBEWA WACCE A TURANCE AKE KIRA DA OKRA KO LADYFINGER TAKE DA AMFANI GA LAFIYAR JIKIN MU?
Masana sunyi bayani sosai game da ruwan kubewa a jikin dan adam wanda kusan mutane da dama basu san amfanin ta ba bayan na miya da ake da ita, kuma ba kowane yasan cewa ana shan ruwan kubewa ba. To hakika kubewa banda miya da muke yi da ita akwai abubuwa da dama wanda kubewa takeyi a jikin dan adam.
Ga Kadan daga ciki Kamar haka.
Masana kiwon lafiya sun ce shan ruwan kubewa yana rage nauyin jiki, yana maganin ciwon sukari, kula da cholesterol, kuma shan ruwan yana maganin cututtukan zuciya, da sauran abubuwa da dama wanda baza mu iya lissafo su a wannan lokacin ba.
Kamar yadda masana ilimin ya'yan itatuwa ke fadi shan miyar kubewa da ruwan ta a kullum da safe yana kare mutum daga matsaloli daban-daban na lafiya.
Kubewa ta ƙunshi furotin, mai, fiber, carbohydrate, calcium, phosphorus, iron, magnesium, potassium, sodium. Kubewa kayan lambu ne mai inganci wanda yake da kyau ga lafiyar jiki gabaɗaya. Kuma shi wannan ruwan idan mace tana yawan amfani dashi zataga yadda jikinta zai canja sosai domin yana karawa mata lafiya, sha'awa da karin ruwan ni'ima.
Karanta -Maganin ciwon sanyi na maza da mata
Yadda ake hada ruwan kubewa
(1) Da farko, za'a ɗauki matsakaitan kubewa Kamar 4-5 a wanke su da kyau.
(2) sai a yayyanke kowacce a raba ta gida hudu waɗannan yatsun hannu a kusan kashi hudu.
(3) bayan angama yankawa sai a Samu cup Mai kyau a zuba a ciki
(4) a zuba ruwa lita 1 zuwa 1.5 daya a cikin cup din
(5) Bayan haka sai a rufe cup din da murfi mai kyau a barta ta jiku
(6) abar kubewar a cikin ruwan tayi Kamar tsawon awanni 8 zuwa 24
(7) bayan haka sai a cire kubewar daga cikin cup din idan ta gama jikuwa
(8) Bayan anyi hakan sai a shanye wannan ruwan, sai dai bashi da dadin sha, amma idan zaki ringa yin hakan duk bayan kwana 5 zakiyi mamaki sosai.
Kuma shi wannan ruwan na kubewa bawai sai iya mata ne kadai zasu sha ba maza ma na iya shan sa domin karin lafiya.
Ga wannan video ku kalla domin ku Kara jin bayanin yadda zaku sarrafa ruwan kubewa