HUKUNCE_HUKUNCEN HAILA GA MAI AZUMI



HUKUNCE_HUKUNCEN HAILA GA MAI AZUMI


Tambaya 1

Idan mace ta sami tsarki bayan fitowar Alfijir, Shin zata kame baki tayi Azumin wannan yinin? Ya zamana  ta azuminci wannan yinin? ko Kuma ramuwar wannan yinin yana kanta, bayan ta kuma kame bakinta??


 Amsa: 

Idan mace ta sami tsarki bayan fitowar Alfijir malamai suna da maganganu guda biyu gameda kame bakinta a wannan yinin;

(1) Magana ta farko: 

Hakika an dora mata kame baki a ragowar wannan yinin, sai dai shi (Kame bakin) ba za'a kirga mata shiba, wajibine sai ta rama azumin wannan yinin. Wannan shine fitaccen zance a Mazhabar Imamu Ahmad Allah yayi masa rahama amen.


(2) Magana ta biyu:

 Hakika ba'a dorawa mace kame bakin ta ba na ragowar wannan yinin ba, saboda azumi acikin wannan yinin bai halarta a gareta ba, kasancewar a farkonsa tana cikin haila, dan haka azumin bai inganta mata ba, kame bakinta bashi da wani fa'ida, wannan lokacin, lokacine da bashida wani hurumi agurinta, saboda an umarceta da taci ta sha a cikin farkon ranar, kai barima an haramta mata azumtar sa a farkon Ranar.

Azumi a Shari'a shine: 

Kamewa daga ciye_ciye da shaye_shaye dan bautawa Allah mai girma da buwaya daga fitowar Alfijir har zuwa faduwar rana.

Wannan zance kamar yadda kake ganinsa shine zance mafi inganci daga cewa sai an kame baki,

    Abisa zantukan duka biyu sunyi ittifaƙi akan  wajabta mata rama azumin  wannan yinin".


 المصدر :

[ ٦٠ سؤالا في أحكام الحيض والنفاس/لفضيلة الشيخ محمد بن صالح العثيمين رحمه الله ص٧].


HUKUNCE HUKUNCEN HAILA GA MAI AZUMI KASHI NA BIYU (2)


Tambaya: 

Shin idan al'adar mace ya ɗauke sai tayi wanka bayan fitowar alfijir, sai tayi sallah tayi azumi, shin zata rama azumin wannan ranan??


Amsa:

 Idan al'ada ya ɗaukewa mace kafin fitowar alfijir koda da minti ɗaya ne kuma hakan a Ramadan ne to ya wajaba akanta tayi azumi a wannan ranan, domin tayi azumi tana cikin tsarki, koda kuwa batayi wanka ba sai bayan fitowar alfijir, kamar namiji ne da ya tashi da janaba ajikinsa sawa'un na saduwa ne ko kuma na mafarki, baiyi wanka ba har sai bayan fitowar alfijir azuminsa yana nan babu abinda ya sameshi.

   Aƙarƙashin wannan zanso in faɗakar da mata akan wani abu, idan al'ada ta zowa mace bayan faɗuwar rana kafin tayi sallan magriba, azuminta na nan bai ɓaci ba, koda kuwa yazo matane bayan faɗuwar rana da minti ɗaya, azuminta ya cika"

 المصدر :

[ ٦٠ سؤالا في أحكام الحيض والنفاس/لفضيلة الشيخ محمد بن صالح العثيمين رحمه الله ص٨].



Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post