HADISAN DA SUKE NUNI AKAN FALALAR YA'YA MATA

 


HADISAN DA SUKE NUNI AKAN FALALAR YA'YA MATA

Akwai hadisai masu tarin yawa da suke nuni akan falalan haihuwar ya'ya mata, da kuma darajar da duk wanda ya kula dasu zai samu awurin Allah, zamu kawo kaɗan daga ciki; 


(1) Hadisin Anas Bin Malik Allah ya ƙara masa yarda yana cewa manzon Allah yace "Duk wanda ya kula da ya'ya mata guda biyu ko uku, ko kuma ya kula da yan uwansa mata biyu ko uku har zuwa lokacin da ya rabu dasu (imma ya aurar dasu ko kuma mutuwa ta rabasu) ko kuma ya barsu to zan kasance tareda dashi a Aljannah kamar haka, sai ya nuna yatsansa na tsakiya da mai binta". 

سنن ابن ماجه

 (2) Hadisin Uqbatu bin Amir Allah ya ƙara masa yarda yace manzon Allah yace "Duk wanda yakeda ya'ya mata guda uku yayi haƙuri dasu ya ciyar dasu ya shayar dasu ya tufatar dasu daga cikin abunda Allah ya bashi, to zasu kasance masa garkuwa daga shiga wuta ranar qiyama"

سنن الترمذي

(3) Hadisin Nana Aisha Allah ya ƙara mata yarda tace Manzon Allah yace "Duk wanda aka jarrabeshi da ya'ya mata, sai yayi hakuri dasu zasu kasance masa garkuwa daga shiga wuta".

   🔹 Imam An-Nawayi Allah ya masa rahama yake cewa "Manzon Allah ya ƙira ya'ya mata da jarrabawa ne saboda mafiya yawan mutane suna ƙyamarsu basason haiguwarsu, kamar yadda Allah yace "Idan akayiwa ɗayansu bushara da an haifa masa ya' mace sai ya haɗa fuska yana mai fushi".

(4) Hadisin Abu Sa'eed Al-Khudri Allah ya ƙara masa yarda yace manzon Allah yace "Duk wanda yakeda ya'ya mata guda uku, ko yan uwa mata guda uku, koma guda biyu ne, ya kyautata zama dasu yaji tsoron Allah cikin lamarinsu to yanada Aljannah".

سنن الترمذي

(5) Hadisin Jabir bin Abdillah Allah ya ƙara masa yarda yace manzon Allah yace "Duk wanda yakeda ya'ya mata guda uku, ya kyautata tarbiyarsu, yaji tausayinsu, Aljannah ta wajaba agareshi, sai akace ya manzon Allah koda ya'ya mata biyune?? Sai manzon Allah yace eh koda biyune, sahabi jabir yace da ance koda ɗayane da yace eh koda ɗayane"

 مسند إمام أحمد

 (6) Hadisin Nana Aisha Allah ya ƙara mata yarda tace manzon Allah yace "Babu wani mutum acikin al'ummata da zai kula da ya'ya mata guda uku ko yan uwansa mata guda uku, ya kyautata musu face sun zame masa kariya daga shiga wuta"

🔹Almubarakafuri Allah ya masa rahama yake cewa "Malamai sunyi sabani akan kyautatawa da tazo acikin waɗannan hadisan, shin ta taƙaitune akan kyautatawa na tilas wanda daman haƙƙine na mahaifi akan ya'yansa ko kuma kyautatawa ta ƙarine?? Yace abunda yake zahiri awannan hadisan shine kyautatawa ta musamman wato ɗoriya akan ta wajibi wanda ya dace da shari'a, sannan wannan falala zai sametane idan ya ɗore akan kyautata musu har zuwa lokacin da zai aurar dasu ko kuma zuwa lokacin da zasu wadata daga kyautatawarsa". 


◼️ Mu haɗu adarasi na gaba in sha Allah.



Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post