Gwamnatin Jihar Kano ta musanta labaran da ke yawo cewa sai da ta biya wasu makudan kudade ta bayan fage ga shugaban tawagar kungiyar kwallon kafa ta Super Eagle Ahmad Musa kafin ya amince da komawar sa kungiyar ta Kano Pillars.
Jim kadan bayan komawar Ahmad Musa zuwa tsohuwar kungiyar sa ta Kano Pillars ne labarai suke ta yawo cewa anbiya dan wasan wasu manyan kudade. Sai dai a martanin ta gwamnatin Kano tace Ko kadan babu gaskiya akan wannan zargi.
A jawabin sa da manema labarai mataimakin gwamnan Kano Nasiru Yusuf Gawuna ya shaida cewa babu wasu kudi da suka biya wannan dan wasan. Sannan mataimakin gwamnan ya bayyana Ahmad Musa a matsayin mutumin kirki saboda munsha zama dashi munyi magana tun yana kungiyar sa ta Saudia dake birnin Riyad. Kuma a maganganu da mukai dashi a lokacin ya bayyana min cewa bazai taba mantawa da tsohuwar kungiyar sa ta Kano Pillars ba, hakan yasa har na bashi shawara mai zai hana yadawo gida Nigeria amma bance masa yadawo kungiyar Kano Pillars ba shine ya yanke shawarar dawo wa Kano Pillars a cewar mataimakin gwamnan.