FALALAR KARANTA WASU AYOYIN ALQUR'ANI LOKACIN KWANCIYA BARCI


FALALAR KARANTA WASU SURORI LOKACIN KWANCIYA BARCI

Barkanmu da sake saduwa daku a wannan lokacin. Yau insha Allah zakuji falalar karanta ayoyin Al'qurani a lokacin da mutum zai kwanta bacci

  • Karanta AYATUL KURSIYYU

Manzon Allah ﷺ yana cewa;-

(Idan kazo kwanciya a shimfidarka to ka karanta AYATUL KURSIYYU,Wato

﴿اللّهُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ﴾ bazaka gushe ba kana tare da mai kariya daga Allah,Kuma shaidan bazai kusance ka ba har sai ka wayi gari)

@صحيح البخاري-رقم (3275).


  • Karanta QUL YÃ AYYUHAL KAFITUN


Manzon Allah ﷺ yana cewa;-

(Idan kazo kwanciya shimfidarka acikin dare,to ka karanta QUL YA AYYUHAL KAFIRUN,"قُلْ يَا أيُّهَا الْكَافِرُونَ"sannan sai ka kwanta barci alokacin da ka gama karantata,Domin ita kubutace daga Shirka)

@حسنه الألباني في صحيح الجامع -رقم :(292).


  • Karanta QUL HUWALLAHU da FALAQI da NASI


Daga Nana A'isha رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا,tana cewa,Manzon Allah ﷺ ya kasance,idan yazo kwanciya a shimfidarsa a kowane dare,yana hada tafikan hannuwansa,Sannan sai yayi tofi acikinsu,

sai ya karanta,QULHUWA FALAQI da NASI)

﴿قُلْ هُوَ اللَّهُ أَحَدٌ﴾وَ﴿قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ الْفَلَقِ﴾وَ﴿ قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ النَّاسِ ﴾،

Sannan sai ya shafi abinda ya sauwaqa daga jikinasa,yana farawane daga shafar kai,da abinda yayi saura na jikinsa,yana yin haka har sau ukku)

@صحيح البخاري-رقم : (5017)


  • Karanta suratul ISRA'I da ZUMAR*


Daga Nana A'isha رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا,tace,Manzon Allah ﷺ ya kasance baya kwanciya barci har sai ya karanta *SURATUL ISRA'I da SURATUL ZUMAR*.

@صححه الألباني في صحيح الترمذي -رقم:(2920)


  • Karanta Suratul MULK wato TABARA


 Manzon Allah ﷺ yana cewa;-

(Lallai akwai wata Sura ta Alqurani mai ayoyi guda Talatin,tana neman ceton bawa har sai an gafarta masa,itace Suratul TABARA.....)


Daga Abdillahi bn Mas'ud R.A yana cewa;-

"Wanda ya karanta Suratul TABARA

{تباركَ الذي بيدِه الملكُ}

A kowane dare,Allah zai kare shi da ita daga Azabar Qabari,Mun kasance a lokacin Manzon Allah ﷺ muna kiranra mai tseratarwa.....".

@صحيح الترغيب 1475 صحيح ابن ماجه 3068 صحيح الترمذي 2891 صحيح أبي داود 1400 الألباني 

 

Manzon Allah ﷺ ya kasance yana karanta Suratul TABARA  da Suratul 

SAJADA,akowane dare"

@صحيح الجامع  ٤/٢٥٥ الألباني 

  • Karanta Ayoyi guda biyu na karshen Suratul BAQARA*


Manzon Allah ﷺ yana cewa;-


(Dukkan wanda ya karanta ayoyi guda biyu na karshen suratul BAQARA a kowane dare ta isar masa)* 

@البخاري مع الفتح، ٩/ ٩٤، برقم ٤٠٠٨، ومسلم،١/ ٥٥٤، برقم ٨٠٧، والآيتان من سورة البقرة، ٢٨٥-٢٨٦.


﴿آمَنَ الرَّسُولُ بِمَا أُنْزِلَ إِلَيْهِ مِنْ رَبِّهِ وَالْمُؤْمِنُونَ كُلٌّ آمَنَ بِاللَّهِ وَمَلائِكَتِهِ وَكُتُبِهِ وَرُسُلِهِ لا نُفَرِّقُ بَيْنَ أَحَدٍ مِنْ رُسُلِهِ وَقَالُوا سَمِعْنَا وَأَطَعْنَا غُفْرَانَكَ رَبَّنَا وَإِلَيْكَ الْمَصِيرُ


لا يُكَلِّفُ اللَّهُ نَفْسًا إِلا وُسْعَهَا لَهَا مَا كَسَبَتْ وَعَلَيْهَا مَا اكْتَسَبَتْ رَبَّنَا لا تُؤَاخِذْنَا إِنْ نَسِينَا أَوْ أَخْطَأْنَا رَبَّنَا وَلا تَحْمِلْ عَلَيْنَا إِصْرًا كَمَا حَمَلْتَهُ عَلَى الَّذِينَ مِنْ قَبْلِنَا رَبَّنَا وَلا تُحَمِّلْنَا مَا لا طَاقَةَ لَنَا بِهِ وَاعْفُ عَنَّا وَاغْفِرْ لَنَا وَارْحَمْنَا أَنْتَ مَوْلانَا فَانْصُرْنَا عَلَى الْقَوْمِ الْكَافِرِينَ﴾

Allah ne mafi sani 

 Allah ka bamu ikon da Manzon Allah ﷺ a dukkan rayuwa baki daya. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post