SALLAN DARE (Qiyamul-laili)
- Sallan dare tana sanya ka daga cikin bayi na gari.
- Akwai lada 'boyayya ga wanda yake tsayuwar dare.
- Sallan dare tana d'aga ka zuwa matsayin masu gode Allah.
- Sallan dare tana tseratar da kai daga wuta
- Sallan dare tana d'aga ka izuwa wadanda suke masu biyayya ga Allah
- Sallan dare tana sanya ka kusa da Ubangijin halittu
- Sallan dare lokaci ne na amsa Addu'a
- Ita Sallan dare Sababi ne daga cikin sabubban shiga Aljannah
- Sallan dare tana sanya ka daga cikin wadanda Allah yake son su
- Wanda ya yi tsayuwar dare shida matarsa Addu'ar Annabi s.a.w zata same sa
- Sallan dare tana sanya ka acan saman Aljannah (ka samu gida a saman Aljannah)
- Daukaka/darajan ta mumini shine Sallan dare
- Yana burge Allah ga wani zai yi tsayuwar dare, kuma Allah yana dariya agare shi (dariyan jin dad'i).
- Me tsayuwar dare kusa yake da Allah Ta'ala
- Sallan dare tana warware kullukan shaid'an
- Sallan dare tana sanya ka shiga Aljannah ba tare da zafin wuta ya same ka na.
Wannnan sune kadan daga cikin falalar sallar dare, don haka kada mutum yai wasa da wannan garabasar.
Kuma idan kun karanta kuyi kokarin turawa sauran yan uwa suma su amfana, Allah yasa mudace amen.
Duba littafin (Dariqus-salihin) malam Waheed Abdus-Salam Baliy
Allah Ta'ala ka sanya mu cikin bayi masu wannan ibada mai tsada tare da kyakkyawan niya (Amin)
Tags:
Daga Malamai